Rahotanni daga yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar na cewa masu fashi da makami sun fara addabar yankin da tare hanya, inda sukan kwace dukiyoyi tare da jikkata jama'a da dama.
A lokuta da dama ma, akan rasa rayukan a irin wannan yanayi a cewar matafiya.
“Mutum uku ne suka tare mu, duk da bindigogi a hannunsu, kafin ma mu ba da kudin wasu an ji masu ciwo wasu kuma an bubbuge su.” Inji wani da ya fada tarkon ‘yan fashin a dajin Agadez, wanda ya nemi kada a bayyana sunansa.
Tuni dai hukumomi a yankin suka fara wani taro, bayan da al’umar yankin ta fara korafi kan matsalar ta fashi a yankin na Agadez.
“Mun hadu ne domin mu ga yadda za mu tsayar da wannan lamari, muna bukatar hadin kan jama’a, kowa ya kawo gudunmawarsa.” Inji Muhammed Anako, shugaban Majalisar Mashawarta a jihar ta Agadez.
Masu lura da al’amura na cewa, matsalar rashin aikin yi, na daga cikin dalilan da ke jefa matasa cikin hali na fashi da makami, inda suka yi kira ga hukumomi da su tashi tsaye domin shawo kan wannan matsala.
Saurari cikakken rahoton Tamar Abari domin karin bayani:
Facebook Forum