Wasu kungiyoyin fafutika na gamayyar DCTR a Jamhuriyar Nijar sun bukaci hukumomin mulkin sojan CNSP su gaggauta daukan matakan mayar da kasar kan turbar dimokradiyya kamar yadda Janar Abdourahamane Tiani ya yi alkawali a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a taron manema labarai da suka kira a birnin Yamai.
A sanarwar da suka fitar kungiyoyin, a karkashin jagorancin Issoufou Sidibe, sun fara ne da nuna gamsuwa kan wasu muhimman matakan da suka ce hukumomin mulkin sojan Nijar sun dauka daga lokacin da suka karbi madafar iko.
‘’A fannin tsaro DCTR na goyon bayan hanyoyin da shugaban majalissar CNSP ya maida hankali kansu wato hada hanyar sulhu da hanyar karfafa matakan soja. Sannan ta na ra’ayin karfafa huldar aiyukan soja a tsakanin kasashe makwabta” inji Sidibe.
Kungiyoyin sun jinjina wa gwamnatin mulkin sojan Nijar dangane da yadda ta yi tsayin daka wajen biyan albashin ma’aikata a kan kari duk da takunkuman da kasar ta fuskanta a baya.
A nasa jawabin yayin taron da manema labarai, kakakin DCTR Laoual Salao Tsayabou yace sun ayyana jerin wasu matakan da hukumomin suka dauka a tsawon watanni 15 na mulkin rikon kwarya da suka kira abin a yaba.
To sai dai gamayyar kungiyoyin ta bukaci hukumomin mulkin sojan a kan maganar mayar da kasar kan turbar dimokradiyya kamar yadda aka alkawalta a baya.
Sauari rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna