Wannan al’amari dai da ya faru a tsakiyar ranar Litanin 14 ga watan Disamba a kauyen Ugo ta yankin Tegina a karamar hukumar Rafi.
Lamarin dai ya yi matukar jefa mazauna yankin cikin wani yanayi na tashin hankali da zaman zullimi.
Wani mazauni yankin da ya nemi asakaya sunan shi ya ce suna cikin tashin hankali ganin yada kusan kullum sai maharan sun aukawa yankin na su.
Shugaban Karamar Hukumar Rafi, Alhaji Isma’ila Modibbo, ya ce ko baya ga wannan ma ‘yan bindigar sun yi awon gaba da hakimin Yakila da wasu jami’an kiwon lafiya guda 2 a garin Gabas.
Sannan ya kuma kara da ce ‘yan bindigar sun kona kimanain garuruwa 8 a karamar hukumar tashi duk a ‘yan kwanakin nan saboda haka ya bayyana bukatar ganin gwanmatin jihar Neja da kuma ta Tarayya da su wai wayi yankin cikin hanzari.
Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Neja, domin kuwa duk kokarin samun kakakin ‘yan sandan Wasiu Abiodun ya faskara.
Sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Ahmad Ibrahim Matane, ya ce gwamnati tana sane da lamari kuma tana daukar mataki.
Yanzu dai mutanan yankin sun zuba ido suga irin matakan da gwamnati za ta dauka cikin hanzari domin kawo karshen wannan matsala ta ‘yan bindiga.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Karin bayani akan: Arewacin Najeriya, sojoji, da jihar Neja.