Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Makaranta A Jihar Tilabery


Wasu malaman makaranta da ke fargaba bayan da ‘yan bindiga suka sace malaman makaranta
Wasu malaman makaranta da ke fargaba bayan da ‘yan bindiga suka sace malaman makaranta

Kungiyoyin malaman makaranta a Jamhuriyar Nijer sun fara nuna fargaba bayan da ‘yan bindiga suka abka wata makarantar boko suka yi awon gaba da malamai 2 a wani kauyen jihar Tilabery.

Jami’an tsaron gundumar Makalondi sun bi sawun maharan da nufin kwato wadanan malamai sai dai kawo yanzu ba a gano inda aka shiga da su ba.

A yammacin jiya laraba ne labarin satar malaman makaranta 2 ya fara bayyana a kafafen sada zumunta duk kuwa da cewa lamarin ya wakana ne tun a ranar juma’ar da ta gabata a wani kauyen karamar hukumar Makalondi dake bangaren da jihar Tilabery ke iyaka da Burkina Faso.

Yankin Tilabery na daga cikin yankunan da matsalolin tsaro ke shafar sha’anin ilimi a Nijar yau shekaru a kalla 8 a sanadiyar aika aikar ‘yan ta’addan yankin Sahel dalili kenan da ya sa uwar kungiyar SYNACEB ta malaman kwantaragi ta kasa ta bakin mataimkin sakaren ta Laouali Garba, ta bukaci hukumomi su gaggauta daukan matakan da zasu bada damar dorewar karatu.

Shugaban ma’aikata a ofishin Ministan ilimi da mataimakin magatakardan Ministan da Muryar Amurka ta tuntuba domin jin matsayin hukumomi a game da batun sace wadanan malamai, ba su daga wayoyinsu ba to amma bayanai daga reshen kungiyar malaman kwantaragi a gundumar Makalondi sun ce mahukuntan na bin diddigin lamarin.

Koma bayan sha’anin ilimi wata matsala ce da masana a wannan fanni ke dauka a matsayin wata babbar barazana ga zaman lafiya da ci gaban al’umma kasancewar illoin abin na shafar makomar yara da ‘yan magana ke kira manyan gobe.

A baya, hukumomin Nijar da hadin gwiwar abokan hulda na kasa da kasa sun bullo da wani tsarin cibiyoyin karatu na musamman da ke tattara yaran garuruwa da dama a yankunan dake fama da tashe tsahen hankula wadanda suka hada da Diffa, Tahoua, Tilabery da Maradi.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG