Hare Haren dai da aka kai a kananan hukumomin Muya da Rafi da yammaci zuwa cikin daren Talata, kamar yadda wani mazaunin yankin Muya da ya nemi a sakaya sunansa yace, maharan sun bi gida gida ne a kauyen Kachiwe su na yi ma mazajen garin yankar rago.
A karamar hukumar Rafi kuma maharan sun auka wa gidan sarkin Kagara inda suka hallaka mutane uku. Amma alokacin harin dai sarkin garin, Alhaji Garba Attahiru na biyu baya gari.
Sakataren Gwamnatin Jihar Nejan Alhaji Ibrahim Matane ya tabbatar da kai wadannan hare-hare tare da ba da karin haske akan adadin mutanen da suka samu labarin mutuwarsu.
Ita ma rundunar ‘yan sandan Jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin inda kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas ya ce sun kara tura karin jami’an tsaro a yankunan sannan su na gudanar da bincike akan lamarin.
A yanzu dai akwai kimanin kananan hukumomi biyar da ke makwabtaka da jihohin Kaduna, Zamfara da kuma jihar Kebbi da gwamnatin jihar Nejan ta datse layukkansu na sadarwa, duk a kokarin yaki da ‘yan ta’adda.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: