A jihar Bauchi, hukumar ‘yan sandan jihar ta ba da sanarwar cewa wasu mahara sun kashe mutane uku da kuma raunata wasu karin mutanen, sa’ilin da suka kai hari a kauyen Yadagungumi da kuma Limi da suke Karamar hukumar Ningi.
A tattaunawa da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, Umar Mamman Sanda ta wayar tarho ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce ana bincike don gano mutanen da suka aikatawar da kisan.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, kwamishinan ‘yan sandan ya ce ba a kai ga kama kowa ba.
“Gaskiya muna kan bincike har yanzu, amma na san cewa sun kashe mutum uku a wasu kauyuka.” In ji Kwamishinan 'yan sanda.
A daya hannun, Shugaban karamar hukumar Ningi, Mamuda Hassan Tabla, ya ce maharan sun kawo hari ne kan wani Attajiri, amma kuma ba su same shi ba sai suka bude wuta akan mai gadin gidan da wasu mutanen suka aika da su lahira.
“Alal hakika, jami’an tsaro sun ba da wannan rahoto, kuma tuni muka dukkan bangare na jami’an tsaro don duba yadda za a bullowa abin.
“Ba a kama kowa ba, amma jami’an tsaro za su ci gaba da yin aiki, har sai sun kamo wadanda suka aikata abin.” In ji shugaban karamar hukumar Ningi Tabla.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad: