Masu tayar da kayar baya sun addabi yankunan da kai hare-hare wanda ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, tare da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.
Da yake tabbatarwa wakilin sashen Hausa faruwar lamarin mazaunin yankin, Alhaji Abdu, ya ce masu garkuwa da mutane ne suka afkawa kauyukan da harbe-harbe, wanda lamari da ya zama ruwan dare a yankin.
Kafin wannan hari da yan bangar dake kare al’umommin yankunan sun shiga daji suka sami nasarar ceto wata mata da ‘yarta a hannunsu, tare da kwato wata bindiga mai harbi har 48 daga maboyarsu.
Mazauna yankunan karamar hukumar Alkari na kallon rashin zaman lafiya dake addabarsu na da alaka da ma’adanan arzikin Man fetur da aka gano a jihar Bauchi, hakan yasa suke kira ga gwamnatin tarayya da kai musu agaji.
Hon Yusuf Mohammed, dan Majaslisar Dokokin jihar Bauchi, dake wakiltar Alkaleri, ya tabbatar da kisan mutane 11 a garin Rimi tare da sace dabbobi da kona kashi biyu cikin uku na garin.
Sai dai a bangaren hukumar yan sandan jihar Bauchi, a wata sanarwa da ta fitar ta hannun kakakinta SP Ahmed Wakil, ta ce ta tura jami’anta don fatattakar yan bindigar.
Don Karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.