Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutum 6 a Taraba


kona kauye
kona kauye

Wasu 'yan bindiga sun kashe mutane sama da mutum 6 a yankin Kararr su ka kuma kona wani bangare na wannan yankin tare da tarwatsa al’ummar mazauna yakin na  Kararr da ke karamar hukumar Gasol a jihar Taraba.

Wani dan yankin da abin ya faru a idonsa ya shaida wa Muryar Amurka tare da alkawarin ba za a ambaci sunansa ba cewa da misalin karfe sha biyu da rabi ne ‘yanbindiga suka kawo musu harin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 6 a yankin nasu.

Malan Zakari Adamu Masin wani mazaunin wannan yankin, ya ce ‘yan bindiga sun dade su na addabarsu a kauye tare da yin lalata da ‘yayansu.

Wani mutum da aka kashe
Wani mutum da aka kashe

Bala Bobbo Gomna, haifaffen kauyen Kararr ne a karamar hukumar Gasol a jihar Taraba ya kuma tabbartar da cewa 'yan bindigar sun dade suna cin karensu ba babbaka a kauyen da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.

Ardo Kiri da ke zama shugaban Sullubawa na karamar hukumar Gasol ya ce a yanzu haka dai su na mawuyacin hali domin ba su da tudun dafawa rana zafi inuwa kuna.

A nasu bangaren jami’an ‘yansanda na jihar Taraba ta bakin kakakin rundunar, DSP Usman Abdullah, ya ce sun hada runduna ta hadin gwiwa domin ganin an kawo karshen ‘yan bindigan a jihar Taraba baki daya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
XS
SM
MD
LG