Jihar Neja dai na daya daga cikin jihohin Nigeria da ke shan bakar ukubar ‘yan fashin daji inda ko a safiyar ranar Laraba suka hallaka mutun guda tare da jikkata wasu da kuma yin garkuwa da mutane sama da goma.
Rahotanni daga yankin Zungeru ta karamar hukumar Wushishi na nuna cewa maharan a kan babura kimani 130 dauke da manyan bindigogi sun kuma tattara shanu masu yawa, lamarin da ya yi matukar tayar da hankalin mazauna wannan yanki.
Wani mazaunin garin na Zungeru da ya bukaci a sakaya sunan shi yace yanzu al’ummomin da ke zaune a sauran garuruwan dake yankin na ci gaba da tserewa domin tsira da rayukkansu.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sandan jihar Nejan a kan wannan sabon harin, domin kuwa kokarin samun kakakin ‘yan sandan Wasiu Abiodun ya ci tura.
Amma Gwamnatin jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin, kwamishinan tsaron cikn gida na jihar Neja Janar Abdullahi Garba Mai ritaya ya ce duk da yake basu gama tantance barnar da ‘yan bindigan suka yi ba amma tuni aka kara tura karin jami’an tsaro a wannan yanki.
Da yake bayani a kan batun ‘yan bindigan da gwamnatin jihar Kaduna ta yi sulhu da su suna shigowa jihar Neja ya ce a jihar Nejan ma suna daukan matakin dakilesu.
Ayanzu dai mazauna wadannan yankuna na cike da fatar kawo karshen tashin hankalin wadannan mahara da aka share shekaru suna gallaza wa jama’a.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasır Batsari:
Dandalin Mu Tattauna