Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Bam Ya Hallaka Sojojin Pakistan 6


Wasu sojojin Pakistan a kan iyaka
Wasu sojojin Pakistan a kan iyaka

Wani harin da aka kai a kudu maso yammacin Pakistan ya yi sanadin mutuwar sojoji shida, ciki har da wani manjo, baya ga wadanda su ka kuma ji raunuka, a cewar wasu jami’an soji.

Wata takardar bayanin soji ta jiya Jumma’a ta ce mummunan harin, wanda aka kai a lardin Baluchistan, an auna shi ne kan wata tawagar soji, a tazarar kilomita 14 daga kan iyakar Iran.

Sojojin na kan hanyarsu ce ta komawa sansaninsu bayan gudanar da wani sintirin da su ka saba yi wanda ya hada da duba wasu hanyoyin da ‘yan ta’adda kan yi amfani da su yankin mai cike da tsaunuka da sauran yanayoyi marasa kyau yayin da wata motar sintiri ta hau kan wani bam, a cewar bayanin. Nan take dai babu wanda ya yi ikirarin kai harin.

Lardin, wanda ke da arzikin ma’adinai, wanda kuma ya fi girma a kasar ta Pakistan, ya sha fama da aika aikar ‘yan tawayen Baluch na tsawon shekara da shekaru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG