A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta da suka hada da WhatsApp a Kamaru, an nuna wasu malamai goma suna rokan ‘yan awaren harshen Inglishi da ke dauke da makamai.
Mata tara da namiji gudan da aka sacen sun ce suna koyarwa ne a makarantar nakasassu da ke Ngomham wata unguwa a Bamenda babban birnin yankin Arewa maso Yamma na Kamaru.
A yau Juma’a ce rundunar sojin Kamaru ta tabbatar da cewa ‘yan awaren sun yi garkuwa da malaman kuma kakakin ‘yan tawayen ya dauki alhakinsu.
Mataimakin babban hafsan tsaro na kungiyar tawayen Ambazonia Defence Forces, Capo Daniel, ya ce sun dauke malaman ne saboda rashin rufe makarantar gwamnati.
"Mun nemi taimako don samar da wasu cibiyoyin ilimi don baiwa yaranmu 'yancin samun ilimi, ciki har da nakasassu na Ambazonia," in ji shi.
Tun a shekara ta 2017 ne 'yan tawayen ke fafatawa a yankunan yammacin kasar domin kafa kasa mai cin gashin kanta da suka kira "Ambazonia" daga mafi yawan masu harshen Faransanci na Kamaru.
Gwamnatin Kamaru ta yi Allah-wadai da sace-sacen da aka yi, inda ta kira harin 'yan aware na baya-bayan a matsayin ‘hari kan ilimi.’
Makarantar Firamare ta Gwamnati na Ngomham din tana koyar da kurame, bebaye, da yara da ke da nakasa tare da wasu ɗaruruwan mutane.
Kungiyar malamai ta kasar Kamaru, Valentine Tameh, ta ce yaran na matukar fargabar zuwa aji tun lokacin da aka sace malamansu.
Tameh ta ce tun lokacin da aka fara rikicin ‘yan awaren sun kashe ko kuma sace malamai akalla 300 a yankunan da ake amfani da harshen Ingilishi.
Rikicin ya barke ne bayan shekara ta 2016, lokacin da malaman harshen Ingilishi da lauyoyi suka yi zanga-zangar nuna adawa da wariya daga hanun wanda ake zargin yawancin masu magana da harshen Faransanci ne.