Ministan Tsaron Kamaru ya kai ziyara kan iyakar arewacin kasar da Najeriya, inda aka kashe sama da mutane 30 ko aka raunatasu a wannan makon a arangamar da suka yi da masu tsattsauran ra'ayin Islama.
Ministan Tsaron Kamaru Joseph Beti Assomo, ya jajantawa sojojin Kamaru 14 da fararen hula hudu da suka ji rauni a asibitin sojoji a Maroua.
Maroua tana cikin Arewa Mai Nisa ta Yankin Kamaru, kimanin kilomita 80 daga jihar Borno ta Najeriya, inda kungiyar Boko Haram ta ke.
Assomo ya ce 'yan kasar Kamaru da shugaba Paul Biya suna cikin alhini tare da iyalan sojojin 14 da Boko Haram ta kashe a iyakar arewaci da Najeriya.
Kamaru wacce ke makwabtaka da Najeriya ta jima ita ma tana fama da matsalar mayakan Boko Haram.
Baya ga haka tana kuma fama da matsalar hare-haren 'yan aware a arewacin kasar.
Wadannan al'amura sun kara dagula matsalolin tsaron kasar wacce Faransa ta rena.