Sun roki gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka masu domin irin halin da suka shiga tun lokacin da suka dawo jihar ba tare da kayansu ko dukiyoyinsu ba. Rikicin Afirka Ta Tsakiya yayi sanadiyar tasowarsu.
'Yan gudun hijiran sun yi kiran ne lokacin da suke karbar wani tallafi daga gidauniyar uwargidan gwamnan jihar Borno Hajiya Nana Kashim Shettima wanda babban jami'in gidauniyar Alhaji Muhammed Bello ya wakilta domin rabawa 'yan gudun hijiran wani tallafi da uwargidan gwamnan ta basu na kayan abinci.
'Yan gudun hijiran dai da suka kai wajen kimanin dari hudu dukansu 'yan asalin jihar Borno ne. An haifi wasunsu a kasar Afirka Ta Tsakiya wasu kuma an je dasu ne tun suna 'yan kanana amma rigingimun kasar suka tilsata masu dawowa gida. Mafi yawansu basu da wani abun yi kuma basu da wani jari a hannu.
Wakilin Muryar Amurka ya samu ya zanta da wasu daga cikin 'yan gudun hijiran akan yadda suka samu kansu a kasar da suka guje ma suka dawo jihar Borno. Mai Abacha yace suna godiya domin an taimakesu. Amma yace yawancinsu suna gidan haya kuma basa iya biyan kudin hayan domin basu da aikin yi. Sabili da haka suna neman taimako.
Tun kimanin watanni hudu ko biyar da suka iso Borno ba'a taba basu wani taimako ba sai wannan karon. Shi Mai Abacha yana da 'ya'ya tara kuma ya kwashe wajen shekaru talatin a Afirka Ta Tsakiya. Ita ma shugabar matan da suka gudo tace yaki ne ya korosu daga kasar Afirka Ta Tsakiya. Iyayensu suka haifesu a can. An kone gidajensu an kuma kwashe dukiyoyinsu.
Shugabar matan ta godewa gwamnan Borno domin tun da suka shiga jihar babu wani dan siyasa ko attajiri da ya je ya gansu saidai gwamnan wanda ya gana dasu cikin sa'o'i arba'in da saukarsu a Maiduguri. Tun daga lokacin gwamnati ta dauki nauyin cinsu da shansu tare da basu sabulun wanka kafin a sallamesu da abun da Allah Ya sawaka.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.