Marayun da suka samu tallafin sun fito ne daga garuruwan Minna, Bidda da kuma karamar hukumar Kontagora.
Tallafin ya fito ne daga wata gidauniya mai suna Rahama Foundation da gwamnatin jihar Neja da kuma kungiyar IZALA mai gabatar da wa'azin addinin Musulunci a Najeriya
Dr. Muhammed Sani Ashir na jami'ar Bayero dake Kano da kungiyar IZALA ta turo jihar Neja domin gabatar da wa'azin Ramadan yayi karin haske akan dalilinsu na tallafawa marayun. Yace idan an barsu ba'a kula da rayuwarsu ba ta fuskar suturarsu da abincinsu da iliminsu to za'a samu matsala dasu nan gaba. Idan sun girma ba tarbiya to an shiga wahala ke nan. Suna iya zama 'yan daba ko barayi ko 'yan ta'ada. Yakamata a kula dasu su ma su rayu kamar yadda kowa ke rayuwa.
Malam Awal Kiki mataimakin sakataren tantance marayun a Kontagora ya bayyana yadda suka zakulo marayun da aka tallafawa. Bisa ga hadin kan malamai da kwamitin da aka kafa aka zakuo marayun.
Marayun da suka samu tallafin sun bayyana jin dadinsu.
Ga karin bayani.