Shugaban Hukumar Kula da yaki da cutar Kanjamau ko AIDS da ake kira NACA a takaice Aliyu Gambo, ya ce babban kalubalen da hukumar ke fuskanta a yanzu shi ne, yawancin kasashe irin su Amurka da ke bada tallafi domin yaki da cutar sun janye tallafin da suke bayarwa. Saboda haka kasar tana fama da karancin kudade don gudanar da yin yawancin ayyukan da ta ke yi, domin sakamakon janye kudaden ya kai har ana samun adadin mutane da yawa da ba sa samun shan magani.
To duk da wannan kalubalen dai masu dauke da cutar sun ragu daga miliyan uku zuwa miliyan daya da rabi a sakamakon kokarin da Gwamnatin Tarrayyar Najeriya ta ke yi wajen shawo kan matsalar tun daga shekara 2015 zuwa yanzu.
Su ma dai masu Kungiyoyin da ke tallafawa masu dauke da cutar irin su Komred Danjuma Abdullahi na kungiyar Umma Support For HIV AIDS, ya ce lallai ana samun damuwa musamman in an je neman magani a asibitocin kasar, abinda ya ke bukatar ganin gwamnati ta yi hobbasa wajen taimakawa don a sami sauki cikin gaggawa.
Majalisar Wakilan Najeriya ta ce tana da labarin janyewar kasashe irin su Amurka amma majalisar tana kokarin ganin an ja hakanlin kasashen wajen dawo da tallafin tun da har ana samun raguwar kamuwa da kwayoyin cutar a yanzu.
Abin jira a gani shi ne yadda Hukumar Yaki da cutar za ta hada hannu da majalisar dokokin kasar domin cimma wanan buri.
Ga karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.
Facebook Forum