Biyo bayan sa hannu da matasan sa-kan Civilian JTF suka yi a fafatawar da ake yi da mayakan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, masana sun ce hakan ya taka rawa wajen samar da kwanciyar hankali a wannan yankin.
Makwabciyar kasar Kamaru ita ma ta dauki wannan matakin. Alhaji Ceini, basaraken Crenewa a Kamaru, ya ce da kadan-kadan jama’ar gari suka fara bin tsarin amma yanzu suna kokarin aiki dare da rana don sa ido a gari.
Aboube Wargazen, shugaban hukumar ne a Diffa, ya ce su ma suna da jami’an sa-kan amma ba sa daukar makamai, sojoji kadai ke daukar makamai.
Ambasada Zanna Bukar Kolo, jakadan Amurka a kasar Chadi ya ce duk da cewa ana samun nasara da mayakan boko haram a wannan shiya ya kamata a sani yakin na da wuyar sha’ani.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum