Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Joe Biden, wanda ya shahara a fagen siyasar Washington na kusan rabin karni, an yi hasashen cewa ya yi nasarar shugabancin Amurka kuma ya kasance za a rantsar da shi a 20 ga watan Janairu.
Yadda Wasu Amurkawa Su Ka Yi Murna, Wasu Kuma Su Ka Nuna Bacin Rai Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasar
- Binta S. Yero
- Steven Ferri
Mutane sun mayar da martani bayan kafofin yada labarai sun sanar cewa dan takarar shugabancin Amurka na Democrat Joe Biden ya lashe zaben shugaban kasar Amurka na 2020

9
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattijai Chuck Schumer (D-NY) na murna yayin da kafofin yada labarai ke sanar da cewa dan takarar shugabancin Amurka na Democrat Joe Biden ya lashe zaben shugaban kasar na 2020, a gundumar Brooklyn ta New York City, Amurka, Nuwamba 7, 2020.

10
Magoya bayan Shugaban Amurka Donald Trump sun yi gangami a wajen ginin Majalisar Dokokin Jihar Pennsylvania bayan kafafen yada labarai sun bayyana Biden a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban Amurka na 2020, a Harrisburg, Pennsylvania, Amurka, Nuwamba 7, 2020

11
Bikin magoya bayan Biden a Fadar White House

12
Amurkawa na bikin zaben sabon shugaban kasa Joe Biden
Facebook Forum