Akalla mutane 50 suka mutu wasu 150 kuma suka jikkata a lokacin da wani jirgin kasa mai gudun tsiya da ya fito daga wata hanyar karkashin kasa ya kauce layinsa a gabashin Taiwan ranar Juma’a.
Daruruwan pasinjoji ne ke cikin jirgin na kamfanin Taroko Express da ke kan hanyarsa ta zuwa Taitung, wani birni a kudancin Taiwan. Jirgin na kan tafiya ne daga birnin New Taipei kafin ya kauce layinsa a kusa da Hualien a gabashin gabar tekun kasar. Wata motar aikin gini da aka ajiye ce ta gangaro daga wani tsauni ta yi karo da jirgin mai gudun tsiya, a cewar rahotanni.
Cikin wadanda suka mutu har da direban jirgin da mataimakinsa. Wasu da yawa da suka tsira daga hadarin ana jinyarsu a asibitocin da ke kusa. Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Wasu rahotanni da suka bazu sun ce kusan pasinjoji 500 ke cikin jirgin, fiye da kujeru 376 na jirgin, abinda ke nufin pasinjoji da yawa a cikin jirgin suna a tsaya ne a lokacin da hatsarin ya faru.
Daruruwan pasinjoji sun makale a cikin jirgin kasan a hanyar karkashin kasar bayan aukuwar hadarin amma da misalin karfe 6:30 da yamma agogon yankin babu wani pasinja da ya rage a cikin jirgin. An ga ma’aikatan jinkai sun kwashe gawarwaki a wurin da hadarin ya faru.
Wasu da suka shaida lamarin sun ce har zuwa karfe 8:00 na yammacin ranar Juma'a an ga ma'aikata na aiki a wurin da hatsarin ya faru.