Jihar Adamawa na cikin jihohin da bala’in Boko Haram ta fi shafa, kuma ko a yan kwanakin nan an samu hare hare musamman a yankin Madagali, baya ga baiwa yara bama bamai cikin rashin sani.
Haka nan wannan na zuwa ne yayin da ake haramar yin bukukuwan sallah.
Festus Mana Abubakar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa y ace za’a tsaurara matakan tsaro da kuma kara baza ‘yan sanda domin kare rayuka. Yace sun shirya domin a yi bukukwan sallah cikin kwanciyar hankali da walwala. Saboda haka sun nemi hadin kai daga jama’a ta sanar dasu duk abun da basu yadda dashi ba. Kodayake ya ki ya fadi adadin ‘yan sandan da suka tanada, Festus y ace zasu baza jami’ansu cikin kowane lungu da sako.
Shima da yake karin haske jami'in hulda da Jama'a na rundunan tsaron farin kaya ta civil defense Suleiman Baba cewa ya yi suma al'umma suna da rawar da zasu taka. A nasu bangaren y ace sun dauki wasu matakai. Mataki na farko y ace dole zasu tantance mutanen da zasu je wuraren ibada. Zasu sa tazara tsakanin wurin ibada da wuraren da za’a ajiye ababen hawa. Haka ma zasu yi a duk wuraren da ake zuwa shakatawa lokacin bikin sallah. Wuraren da mutane zasu shiga kofa daya za’a bari inda za’a tantance duk masu shiga da fita
To sai dai kuma al'umma Madagali da Michika da su aka fi kaiwa hari, sun bayyana irin halin fargabar da suke ciki. Mr Adamu Kamale Dan majalisar wakilai ne dake wakiltar yankin yace akwai bukatar kai musu dauki a wannan lokaci na Bukukuwan sallah.
Ya ce sai an samu zaman lafiya ne mutane zasu ji dadin rayuwa da yin bukukuwa. A yankinsa ya ce ba dadi suke ji ba saboda koyaushe aka ce ana bikin sallah ko aure mutanensa fargaba su keyi domin ba zato ba tsammani sai a ga gari ya rude sanadiyar hare-hare na ‘yan ta’adda dake keta yankunasu akai akai.
Adamu Kamale yace jami’an tsaro nada babban aiki da zasu yi a yankin Madagali da Michika. Ya bukaci sojoji su shiga gefen dajin Sambisa dake kusa dasu, domin su san abun dake faruwa.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum