Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Ranar Dimokradiyya Ta Duniya A Ghana


Majalisar Dokokin Ghana
Majalisar Dokokin Ghana

Bikin na zuwa ne yayin da tsarin dimokradiyya ke fuskantar kalubalen juye-juyen mulkin soji a yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka.

Ana sadaukar da wannan muhimmiyar rana ce don yin nazari kan yanayin dimokradiyya a duniya; inganta ta; da kuma kiyaye ka’idojin da ke tattare da ita.

Sai dai karuwar juyin mulkin da aka yi a wasu kasashen yammacin Afirka da kuma kasar Gabon a Tsakiyar Afirka sun bayyana kalubalen da wannan tsarin gwamnati ke fuskanta a Afirka.

Dimokradiyya ta ta'allaka ne akan muhimman dabi'u da suka hada da 'yanci fadar albarkacin baki, mutunta 'yancin dan adam, da gudanar da sahihin zabe akai-akai.

Bisa la’akkari da muhimmancin wadannan, Majalisar Dinkin Duniya, a yayin babban taronta a shekarar 2007, ta ayyana ranar 15 ga watan Satumba a matsayin ranar dimokradiyya ta duniya.

Ghana ta kasance kasa ta biyar a jadawalin ma’aunin karfin dimokuradiya a Afirka na 2023, bayan kasashen Mauritius, Botswana, Cape Verde da Namibia.

Duk da cewa ana samun tangarda a wasu bangarorin dimokradiya a kasar, amma duk da haka Ghana na iya kokarinta, in ji Al-Hassan Sulaiman Bello, mai bincike kuma manazarci kan harkokin siyasa.

Ya ce "ana canja gwamnati ba da tashin hakali ba. Kuma idan aka yi zabe, aka samu banbancin ra’ayi, ana zuwa kotu domin raba gardama. Amma, duk da haka, dimokuradiyya tsari ne da ake bi, ba abu bane da za a same shi dafaffe a zauna a ci ba, sai an bi tsari. Domin haka, ana samu matsaloli a wasu bangarorin.

Sai dai Issah Abdul Salam, sakataren jam’iyar CPP na yankin Ashanti yana ganin dimokradiyar Ghana na fuskantar matsaloli, musamman a baya-bayan nan.

Ya ce mambobin majlisar dokokin kasa suna ajiye kishin kasa a gefe su bi son ra’ayinsu ko na jam’iyarsu. Ya kamata a dauki matakin da al’umma za ta samu kwarin gwuiwa ga dimokuradiyar kasar.

Taken bukin dimokuradiyar bana shi ne, ‘Karfafa Manyan Gobe’, wato matasa ba kawai shugabannin gobe ba ne, amma suna taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da dimokuradiyya gaba a yau, da kuma tabbatar da cewa an shigar da muryoyinsu cikin shawarwarin da ke da tasiri a rayuwarsu.

Sadat Hamisu Barko, wani matshin dan siyasa ya ce, lallai matasa na da matukar tasiri a dimokradiyar Ghana.

"Misali, idan mun dubi shugabancin manyan jam’iyyun siyasa kasar, matasa na da yawa a ciki. Sun samu karbuwa kuma suna taimakawa jam’iyyun."

Ya kara da cewa, a jami’un ilimin kasa, matasa na gudanar da siyasa yadda babbar jam’iyar adawa ta NDC da kuma jam’iya mai mulki ta NPP na da wakilci a ciki.

Tun daga shekarar 1992, kasar Ghana ta gudanar da zabukan jam'iyyu da dama, kuma ta yi nasarar mika mulki cikin lumana tsakanin manyan jam'iyyun siyasa biyu, wato NDC da NPP.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG