Dattijon jam'iyyar babbar adawa ta PDP Alhaji Lamido Umar Citere shi ya fada haka a firar da ya yi da manema labarai.
Alhaji Citere yace lokacin adawa ya wuce yayinda kasar ke neman durkushewa saboda illar zagon kasa.
Alhaji Citere yace a nemo kwararru wadanda suka iya aiki, idan ba haka ba shugaban yana cikin mawuyacin hali. Ya kira 'yan arewa da sauran 'yan Najeriya su taimaki shugaban idan kuma basu kawo masa doki ba kowa ransa zai baci. Yace idan aka bari Buhari ya kasa kowa zai ji a jikinsa. Yace wajibi ne Shugaba Buhari ya nemo mutane nagari da suka iya aiki koina suke.
Shi kuma tsohon dan rajin sauyin lamuran mulki daga wadanda ya kira 'yan jari hujja Yau Ciroman Bakan Daura yace kalubale ya yi yawa ne a bangaren shari'a. Yace 'yan majalisa da fannin shari'a ya kamata su fitar da wadanda suka sace kudin kasar suka kai talaka suka baroshi. Yace a duba gwamnonin arewa na jihohi goma sha tara da kyar a samu wadanda basu wawure kudin jama'a ba. Duk da haka watakila jihohi uku ko hudu ne suka kai gwamnoninsu kotu akan sun saci kudade. 'Yan majalisa sun yi shiru domin 'yanuwansu ne masu cin hanci.
Yace idan har fannin shari'a ba zaI taimakawa shugaban kasa ba a dawo da kudaden da aka sace a yiwa talakawa aiki dasu, yace shi da mutanen Najeriya zasu fantsama cikin zanga zanga a duk fadin kasar.
Amma wani tsohon dan majalisar wakilai Barrister Ibrahim Bello nada kwarin gwuiwar lamura zasu daidaita. Yace dole ne da mutanen da da na yanzu a hada kai a ga abun da za'a iya yi. Yace matsalolin kasar nada yawa saboda haka dole ne a hakura a cigaba da addu'a.
Ga karin bayani.