Gwamna Abubakar Sani Bello wanda yake jawabi a wajan rufe gasar karatun Alkur’ani da kungiyar izala ta shirya a Minna, ya ce akwai abin takaici akan lamarin wai ace idan mutun zaije wani gari a cikin kasarsa amma hankalinsa atashe saboda su shugabanni da ‘yan siyasa basu so wani ya rasa ranshiba ta hanyar hukuntawa.
Gwamna Bello ya ce gwamnan jihar Filato ya na iya kokarinsa amma akwai bukatar ci gaba da yin addu’o’i ganin yadda asiri ya fara tonuwa da har ta kai ga angano wani katon kududdufin da ake jefa gawarwakin jama’a idan ankashe su.
A yanzu haka dai gwamnan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin a kwashe ruwan kududdufin.
Shugaban Majalisar malamai ta kungiyar izala mai hedikwata a Jos Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce rashin hukunta wadanda aka samu da laifi ne yasa rikicin na jihar Filato yaki ci yaki cinyewa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum