Kungiyar ta bayyana haka ne a wajen wani taron karawa juna sani da ake shiryawa domin wayar da kan ma’aikata kan matakan kula da lafiyarsu.
Bisa ga cewar kwararru, mutane suna kamuwa da cutuka dabam dabam da za su iya karewa idan suna kula da yadda suke rayuwa da ya hada da abincin da suke ce da kula da lafiyarsu da kuma halin rayuwarsu ta yau da kullum.
Kwararrun sun bayyana cewa, a halin yanzu sama da mutane miliyan 370 ne suke dauke da ciwon suga, kuma yana yiwa adadin ya kai miliyan 500 a shekara ta dubu biyu da ashirin da uku idan ba a dauki matakin shawo kan matsalar ba.
Suka ce mutane da suke fama da ciwon suga sukan fuskanci matsalar bugun zuciya ko kuma matsalolin da suka fi haka muni, da zai kai ga mutuwa.
Kwararru sun bada shawara cewa, jama’a suna bukatar kula da abincin da suke ci a wuraren ayyukansu musamman wadanda suke bakin aiki na lokaci mai tsawo wadanda sau da dama sukan fita su sayi abinci da yake zama da illa ga lafiyarsu idan suka ci na lokaci mai tsawo.