Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Jihohin Dake Samun Bullar Polio Ya Ragu A Najeriya


Kwamitin “Polio Plus” a Najeriya yace yanzu babu kwayar cutar Polio a kashi 99 cikin 100 na Najeriya.

Ana saura kasa da kwanaki 500 kafin cikar wa;adin da Najeriya ta dibar na kawo karshen yaduwar kwayar cutar Polio, Kwamitin “Polio Plus” na Najeriya yace a yanzu babu wannan kwayar cuta ta Polio a kashi 99 cikin 100 na sassan Najeriya.

Kwamitin na “Polio Plus” wanda kungiyar Rotary International ta kafa da tallafin dala miliyan 120, shi ne wani sashi mai zaman kansa mafi girma na kasa da kasa dake tallafawa yunkurin gwamnati na kawar da Polio.

Alkaluman Kwamitin sun nuna cewa an samu raguwar yawan masu kamuwa da cutar, inda ya zuwa 7 Agusta, aka tabbatar da mutane 43 ne suka kamu da kwayar cutar in an kwatanta da mutane 65 da suka kamu da ita daidai wannan lokaci a shekarar 2012.

Haka kuma, an samu raguwar jihohin da aka ga bullar cutar Polio a bana da jihohi hudu. Ma'ana, a bana an samu bullar cutar ce a jihohi 9 kawai, maimakon a jihohi 13 da aka samu bullar cutar a 2012.

An samu rahoton bullar cutar Polio ta baya-bayan nan ranar 14 Yuli a yankin karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Babbar matsalar da ake fuskanta a yanzu, ita ce ta yadda za a iya samun kaiwa ga dukkan yara, musamman a jihohin da suke fama da matsalolin tsaro. Saura sun hada da farfagandar karya da wasu ke yadawa kan diga maganin rigakafin cutar ta Polio.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG