Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Gwamnati Ta Tilasta Yi wa Kasuwanni Inshora - Saraki


Bukola Saraki A Wata Tattaunawa Da Reuters
Bukola Saraki A Wata Tattaunawa Da Reuters

"Mafi yawan lokuta ana samun gobara a kasuwanni sakamakon halin ko-in-kula daga wasu mutane, rashin bin tsari a kasuwanni ko yanayin kafa su tare da matsalar wutan lantarki da dai sauran su, wanda kuma ke sanadiyyar karayar arzikin wasu da dama."

Tsohon shugaban majalisar dattawa, sanata Bukola Saraki da kungiyoyin fararen hula a Najeriya sun yi kira ga gwamnatoci a dukan matakai, da su wajabtar da tsarin inshora ga kasuwanni domin rage radadi da dimbin asarar da yawan gobarar da ake samu ke yi ga harkokin tattalin arziki a kasar.

Bukola Saraki da kungiyoyin fararen hulan sun bayyana hakan ne a yayin taron karawa juna sani ta yanar gizo da cibiyar ilimi ta Politeia ta nahiyar Afirka ta shirya karo na biyu a karkashin jagorancin Saraki, wanda aka yiwa take “ tattaunawar ciyar da Najeriya gaba.”

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar yawan gobara a kasuwannin kasar da tasirin hakan ke kara ta’azarra yanayin talauci a tsakanin jama'a.

Kungiyoyin fararen hulan sun bayyana cewa, a lokuta da dama ana samun gobara a kasuwanni ne sakamakon halin ko-in-kula daga wasu mutane, rashin bin tsari a kasuwanni ko yanayin kafa su tare da matsalar wutan lantarki da dai sauran su.

A cewarsu, mafi yawan kasuwanni a Najeriya sun zama gidajen zama ga mutane da yawa, wanda hakan ke nuna yadda talauci ya yiwa kasar katutu sakamakon yanayin matsin tattalin arziki.

Kungiyoyin dai sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa, baya ga samar da jami’an tsaro ga kasuwannin, kada a bari mutane su maida wuraren kasuwancin wajen zama na dindindin, idan ba bukatar aiki ce ta sa mutum zai kwana a kasuwa ba.

Masana da dama a yayin taron sun bayyana cewa fito da ingantaccen tsari, samar da wutar lantarki na bai daya da kuma tsarin rarrabawa tare da yin amfani da hanyoyin samun wutan lantarkin na hasken rana, zai taimaka matuka wajen magance wannan matsalar gobara da ake yawaitar samu a kasuwannin kasar.

Sun kuma lura da cewa, yawancin kasuwanni ba su da tsarin inshora, don haka a duk lokacin da aka sami gobara, ana yin asara mai yawa, lamarin da kuma ke shafar rayuwar ‘yan kasuwa na yau da kullum.

Haka kuma sun ba da shawarar cewa a maimakon ba da tallafin miliyoyi bayan gobara don sake gina kasuwannin, kamata yayi a ba da wadannan kudadden wajen daukar matakan kaucewa wadannan gobarar da kuma samar da inshora ga kasuwanni.

Akan haka suka bukaci gwamnati da ta samar da dokar wajabta tsarin inshora a kasuwannin kasar, tare da bukatar wayar da kan shugabannin ‘yan kasuwa da ma 'yan kasuwar baki daya, wanda suka ce hakan shine babbar hanyar magance matsalolin gobarar da ake fuskanta a kasuwanni.

XS
SM
MD
LG