Da safiyar jiya laraba ne dai wani jirgin ruwa makare da mutane da ya tashi daga jihar Kebbi zuwa Jihar Naija, ya gamu da hatsari, inda ya kife a daidai bayan da ya shigo yankin Wara da ke karamar hukumar mulki ta Ngaski.
Manajan hukumar kula da rafuka ta Najeriya wato NIWA a Yauri na Jihar Kebbi, Yusuf Birma ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce, ya zuwa yanzu ana neman mutane 156 da ba a gani ba, kuma ana fargabar nutsewa suka yi kuma ana zullumin ruwa ya ci su bayan hatsarin jirgin ruwan da ya afku a Jihar ta Kebbi.
Majiyoyi daga jihar Kebbi sun bayyana cewa, a lokacin hatsarin, jirgin ruwan na dauke da fasinjoji 180 da babura kirar Bajaj 30, akan hanyarsu ta zuwa kasuwa a garin Malele da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Naija daga Kebbi.
Hatsarin jirgin ruwan ya auku ne sa’o’i kadan bayan tashinsu kamar yadda Yusuf Birma, manajan hukumar kula da rafuka ta Najeriya wato NIWA a Yauri ya bayyana.
Da yake danganta aukuwar lamarin ga raunin jirgin ruwan, Yusuf Birma ya tabbatar da mutuwar mutum hudu tare da ceto 20 da ran su, a yayin da ake kokarin ceto ragowar mutane 156 da ba a gani ba ya zuwa yanzu.
Rashin ganin sauran fasinjojin da suka shiga jirgin ruwan da ba a kai ga tsamo su da ransu ba da wuri, ya sa ana fargabar mutuwa suka yi, duba da yadda aka samu jinkirin aikin ceton saboda karancin kayan aiki a yankin.
Majiyoyi sun alakanta hatsarin ga yin lodi da ya wuce kima saboda cewa suka yi, baya ga fasinjoji, jirgin ruwan ya kuma dauko wasu kayan masu hakar zinariya da wasu kayan mutane da ke hanyarsu ta zuwa kasuwar kauye.
Ya zuwa yanzu dai, hukumomi na cigaba da gudanar da aikin ceto ne da tsoffin kayan aiki, a yayin da wasu mutane kuma ke amfani da dabarun gargajiya wajen nemo mutanen da ba a gani ba, da suka hada da mata da kananan yara.
Tun ba yau ba ake fuskantar matsalar nutsewar jiragen ruwa, kwale-kwale a tsakanin jihohin Kebbi da Naija sakamakon huldar kasuwanci na yau da kullum a yankin mai sufurin hanyoyin ruwa.
Hakan ya sa masana da masu fashin baki ci gaba da kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen samar da hanyar sufuri mai karancin hatsarin aukuwar irin wannan lamari don tallafawa ‘yan kasa.
Yadda Jirgin Ruwa Ya Nutse Da Sama Da Mutum 100 A Jihar Kebbin Najeriya