Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Kaduna Sun Sa Buhari Bakin Ciki – Garba Shehu 


Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya
Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya

Rahotannin baya-bayan nan sun ce adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a kauyukan karamar hukumar ta Giwa ya kai 38.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana rashin dadinsa dangane da sabbin hare-haren da aka kai a jihar Kaduna wadanda suka yi sanadin asarar rayuka da dama.

Wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar da yammacin ranar Lahadi, ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ba za ta lamunci irin wannan ta’asa ba yana mai nuna alhininsa da aukuwar hare-haren.

“Wadannan kashe-kashe da aka yi na rashin imani a Kauran Fawa, Marke, Ruhiya a mazabar Idasu da ke karamar hukumar Giwa, sun matukar bata wa shugaban rai, gwamnati ba za ta lamunci hakan ba.” Sanarwa ta ce.

Baya ga wadannan hare-hare, har ila yau ‘yan bindiga a cikin mako, sun kai hari a kananan hukumomin Zangon Kataf, Chikun, Birnin Gwari, Igabi da Kaura duk a jihar ta Kaduna.

“Shugaban yana kuma mika sakon ta;aziyyarsa ga gwamnatin Kaduna da al’umar masarautar Zonkwa da kuma iyalan mai martaba Sarki Nuhu Bature, da Agwam Kajju bisa rasuwarsa.”

Shugaban kasar ya kuma kara jaddada cewa, “dakarunmu sun kara kaimi akan ‘yan ta’adda wadanda suke far wa al’uma, suna kwashe musu dukiya, tare da kona gidajensu da yin kisan kan mai uwa da wabi”

“Ya kuma jaddada umarnin da ya bai wa shugabannin jami’an tsaro da masu tattara bayanan sirri kan su yi duk iya bakin kokarinsu wajen ruguza mabuyar ‘yan ta’addan.”

Rahotannin baya-bayan nan sun ce adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a kauyukan karamar hukumar ta Giwa ya kai 38.

XS
SM
MD
LG