Wani alkalin kotun tarayya dake Legas Justice Muhammad Idris ya hana kamfanin samarda wutar lantarki na Najeriya da ake kira PHCN kara farashin da yake ba jama'a wuta.
Alkalin yace kara farashi da kamfanin ke son yi ya sabawa doka saboda bai samarda isasshiyar wutar lantarki da take son ta kara wa kudi ba. Lauya Toluani Adebiyi mai fafitikar kare hakin bil Adama shi ya shigar da karar.
Tuni jama'a suka yi maraba da hukuncin da alkalin ya yanke kamar yadda Malam Abdullahi Abuja na kungiyar masu hakan ma'adanan kasa ya bayyana. Yace yawancin 'yan Najeriya sun yi murna da hukuncin domin a kasar dan Najeriya bai san yadda za'a kwato masa hakinsa ba sai da sabuwar gwamnati ta shigo.
Akwai wasu jihohi ma da aka ce kamfanin samarda wutar lantarki ya mayarwa mutane kudin da ya cajesu saboda an cajesu fiye da abun da ya kamata.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.