Jami'an kasar China, sun fada cewa an sallami duk masu cutar COVID-19 daga asibitocin da ke Wuhan, garin da aka fara samun barkewar cutar, a karshen shekarar da ta gabata.
An saka garin Wuhan, wanda ya ga kusan rabin cututtukan coronavirus na China, karkashin dokar hana fita, mai tsanani, a watan Janairu, kuma aka rufe shi daga sauran sassan kasar.
Ko da yake, duk da an samu sassautawar dokokin sosai, har yanzu ana ci gaba da gwajin mazauna garin akai-akai, don gano kwayar cutar.
Yawancin kasashen duniya, sun dauki matakai daban-daban, da suka hada da hana zirga-zirga a karshen makon da ya gabata, a kokarin shawo kan cutar ta COVID-19.
Amma, a kasar Spain, jami'ai sun kyale yara su fita waje, a karo na farko a cikin makonni shida, wanda ya fara ranar Lahadi.
Facebook Forum