Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa za ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa wanda zai yi bincike kan yanayin kokarinta na shawo kan COVID-19, da kuma irin matakan da su kuma gwamnatoci a duk fadin duniya suka dauka.
Hakan na faruwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi matukar sukar hukumar, inda ya zarge ta da zama 'yar koren China.
A ranar Talata ne ma Amurkar ta bayyana cewa za ta fice daga WHO a cikin tsawon shekara daya.
Tsohuwar frai ministar New Zealand, Helen Clark da tsohon shugaban Liberia, Ellen Johnson Sirleaf sun amince su jagoranci kwamitin, a cewar darakta janar na WHO.
Facebook Forum