A wani abu da ake ganin zai iya daga darajar Najeriya a fannin kere-keren zamani, kasar ta hada wayar salula ta farko.
A ranar Laraba Ministan kasuwanci da saka hannayen jari Adeniyi Adebayo, ya gabatar wa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wayar salular wacce ake kira ITF Mobile wacce kirar Android ce.
A kwanakin baya hukumomin kasar suka bayyana cewa, Najeriyar na shirin kaddamar da waya wacce aka kera a kasar hade da katin waya na sim.
Yayin gabatar da wayar gabanin a fara taron majalisar zartarwar da ake yi mako-mako, Adebayo ya ce cibiyar bincike kan kayan laturoni na hukumar koyar da makamar aiki ta ITF ne ya kirkiri wayar.
“In mai farin cikin gabatarwa da shugaban kasa wannan waya.” Adebayo ya ce, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Hakan na nufin Najeriya mai yawan al’uma kusan miliyan 200, wacce ta fi kowacce kasa yawan jama’a a nahiyar Afirka, ta shiga jerin kasashen da ke hada wayar salula.