Wata babbar tawaga daga kasar Afghanistan ta fara ziyarar aikin kwana daya jiya Lahadi a makwabciyar ta Pakisatan, domin su tattauna wasu muhimman batutuwa, musammam akan batun dake da nasaba da bakin iyaka,da tsaron yankin kasashen.
Jim kadan da bakin na Pakistan suka sauka a babban birnin Islamabad, nan take suka fara tattaunawa da mai baiwa shugaban kasar shawara a harkokin tsaro, Nasser Janjua.
Haka kuma tawagar ta Afghanistan zata gana da babban hafsan sojan kasar Janar Qamar Javed Bajwa.
A farkon wannan watan ne dai kasashen biyu suka samar da wani sabon tsarin da suka kira tsarin Afghanistan da Pakistan da zai samar da sabon tsarin zaman lafiya da hadin kai.Wanda zai kakkabe taaddanci, ya kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban mutanen kasashen biyu.
Facebook Forum