Malam Abdulmummuni Muhammadu shugaban kungiyar dake bada horon yayi bayanin dalilin da ya sa suka dauki nauyin horas da matasan.
Inji Malam Muhammadu yace yau ana cikin wani yanayi inda aka dauki Musulunci tamkar wani addini ne na ta'addanci da kyama da sauransu. Yace alhali kuwa sheri ne ake yiwa addinin.Musulunci ba haka yake ba injishi. Yace Musulunci ya zo da zaman lafiya da son juna da taimakawa juna.
Malam Muhammadu yace ganin irin abubuwan dake faruwa ya sa suka zo su fadakar da 'yanuwansu matasa musulmai domin kada a yaudaresu. Matasa nada gudummawar da zasu kawowa addini idan an fadakar dasu.
Ustaz Rabiu Ismail yace sun fadakar da matasa yadda zasu yi mu'amala da junansu da kuma yin biyayya ga magabantansu da yi masu biyayya akan duk abun da ba sabon Allah ba ne.
Matasan da suka halarci taron sun nuna gamsuwarsu akan yadda aka karantar dasu da kokarin da su matasan ka iya kawowa domin samun zaman lafiya.
Haruna Mamman Bako nada karin bayani.