Da yake magana a wani taro da shugabanni a fannin kudi a birnin Addis Ababa ranar Juma'a, Abiy ya ce gwamnatin tarayya na kokarin tuntubar 'yan tawayen amma da alama rashin hadin kai tsakanin kungiyoyin ka iya kawo cikas.
Ya ce an yi ta kokarin ganin kungiyoyin sun hada kai don "samar da yanayin tattaunawa.
“Amma mun fara tattaunawa da wasunsu; akwai kungiyoyin da suka fara tattaunawa da gwamnati,” a cewar Abiy.
Shugaban dai bai bayyana kungiyoyin mayakan da ake tattaunawa da su ba, da kuma lokacin da aka fara tattaunawar. Hakazalika, ba a bayyana tsarin tattaunawar ba.
Mai magana da yawun daya daga cikin kungiyoyin mayakan Fano da ke fada a yankin Amhara ya musanta yin wata tattaunawa da gwamnati. Fano dai kungiyar mayakan Amhara ce, wadda ba ta da wani tsari na shugabanci kuma akwai kungiyoyi da dama da ke aiki a sassa dabam-dabam na yankin Amhara.
Simeneh Mulatu, shugaban sashen harkokin kasashen waje na kungiyar mayakan Fano a Gojjam, ya shaida wa Muryar Amurka cewa babu wata tattaunawa da aka fara da gwamnati.
Nan take dai ba a ji daga shugabannin sauran kungiyoyin Fano da ke aiki a yankin ba.
Duk da kalaman Abiy, da alama wani jami'in kwamitin samar da zaman lafiya a yankin Amhara da aka kafa a watan Yuni, shi ma bai da masaniya kan rahotannin tattaunawa da wata kungiyar mayaka.
Dandalin Mu Tattauna