Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane Na Bukatar Abinci Cikin Gaggawa A Yankin Tigray Na Kasar Habasha


Tigray
Tigray

Kashi kadan ne kawai na miliyoyin mabukata a yankin Tigray da ke arewacin kasar Habasha ke samun tallafin abinci, a cewar wata sanarwar agaji da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gani.

WASHINGTON, D. C. - Hakan na zuwa sama da wata guda bayan da hukumomin agaji suka dawo da isar da hatsi bayan wani dogon lokaci da aka dakata rabon sakamakon sata.

Tigray
Tigray

Kaso 14 ne kacal cikin 100 na mutane miliyan 3.2 da kungiyoyin agaji suka yi niyyar kai wa abinci a yankin a wannan watan suka samu a ranar 21 ga watan Janairu, a cewar sanarwar da kungiyar Tigray Food Cluster, wadda tarayya ce na kungiyoyin agaji da Hukumar Samar da abinci ta duniya da jami'an kasar Habasha ke jagoranta.

Takardar ta bukaci kungiyoyin agaji da su “kara habaka” ayyukansu nan da nan, tare da gargadin cewa “rashin daukar matakin gaggawa a yanzu zai haifar da matsanancin karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki a lokacin bazara, wanda hakan zai janyo asarar rayukan kananan yara da mata a yankin.

Rashin abinci a Habasha
Rashin abinci a Habasha

Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Amurka sun dakatar da tallafin abinci ga Tigray a watan Maris din shekarar da ta gabata bayan gano wani gagarumin shiri na satar hatsin jin kai. Haka kuma aka kaddamar da dakatarwar ga sauran kasar Habasha a watan Yuni.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun dage dakatarwar a watan Disamba bayan gabatar da sauye-sauye don dakile sata, amma hukumomin Tigray sun ce har yanzu abinci baya kaiwa ga masu bukata.

Satar hatsi a Tigray, kasar Habasha
Satar hatsi a Tigray, kasar Habasha

Kimanin mutane miliyan 20.1 a fadin Habasha na bukatar abinci na jin kai saboda fari, rikici da tabarbarewar tattalin arzikin. Dakatar da taimakon da aka gudanar a baya yanzu ya ƙara haɓaka matakan yunwa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG