ABUJA, NAJERIYA - Bayanin sako yaran makarantar na zuwa ne bayan shafe makonni biyu da ‘yan bindiga da ba’a tantance ko su wanene ba suka yi garkuwa da su a wani lamarin sace yaran makaranta da ya kasance daya daga cikin sace-sacen jama'a mafi girma a Najeriya cikin shekarun baya-bayan nan a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun gwamna Uba Sani na jihar.
An yi garkuwa da kimanin daliban 287 ne a lokacin da ‘yan bindigar haye a kan babura suka bi ta kan makarantarsu, inda suka tafi da su a wani lamari da ya tayar da hankulan jama’a da ya jawo sukar gwamnatin jihar Kaduna da ma na tarayya.
Saidai bayan shafe makonni bayan da ‘yan bindigar suka sace su, an kubutar da ‘yan makarantar, wadanda galibinsu ‘yan shekara 8 zuwa 15 ne.
A cewar sanarwar da ya fitar a safiyar yau Lahadi, gwamna Uba Sani ya bayyana farin cikin samun nasarar ceto yaran yana mai cewa ”Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, ina sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga.”
Gwamnan ya kuma mika godiya ta musamman ga dukkan masu ruwa da tsaki musamman ma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, jami’an gwamnati da jami’an tsaro kan rawar da suka taka wajen kubutar da daliban.
Duk da cewa yawaitar sace-sacen dalibai ya dan ragu a ‘yan watannin baya-bayan nan tun bayan da ‘yan bindiga suka fara kai hari a kan makarantu, sace kananan yaran makarantar Kuriga ya sake tunawa iyaye sace dalibai sama da 200 da aka yi a garin Chibok da ke jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2014.
Idan Ana iya tunawa, ’yan ta’adda da ‘yan bindiga sun sha kai hare-hare musamman ga daliban makaranta, tun daga sace ‘yan matan Chibok a shekarar 2014, zuwa ga sace yaran makaranta a birnin Dapchi na jihar Yobe.
Sace yaran makaranta don neman kudin fansa ya zama ruwan dare inda a watan Disambar shekarar 2020, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnatin maza a Kankara na jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da dalibai kusan 300.
Watanni biyu bayan faruwar lamarin Kankara, a ranar 17 ga watan Fabrairu, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace dalibai 27 da wasu mutane 15 daga makarantar kimiyya ta gwamnati da ke garin Kagara a jihar Neja.
Haka kuma, a wani harin da aka kai da sanyin safiya, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata 317 na makarantar sakandaren mata ta gwamnati a garin Jangebe na jihar Zamfara.
Sannan kuma a karshen watan Mayu wasu gungun mahara dauke da muggan makamai a kan babura suka mamaye garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, inda suka yi harbi ba kakkautawa tare da yin garkuwa da dalibai kusan 150 daga makarantar Islamiyyar Salihu Tanko.
A wannan karon dai Shugaba Tinubu da hukumomin sojin Najeriya, sun kasance sun bada tabbacin cewa za a ceto yaran makarantar Kuriga da abin ya shafa, daga bisani aka sami nasarar kubutar da su.
Masana tsaro dai na kara jadada cewa dole ne a fito da sabbin dabarun kula da dazukan kasar domin samun sauki ga matsalar sace-sace gomman yara daga makarantun su.
Dandalin Mu Tattauna