Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'yan Matan Chibok Sun Shiga Sabuwar Rayuwa a Jami'a


'Yan makaranta mata da suka kubuta daga makarantar sakadaren gwamnati ta Chibok.
'Yan makaranta mata da suka kubuta daga makarantar sakadaren gwamnati ta Chibok.

Yayin da basa zaton abun da zai faru dasu bayan sun koma garinsu na Chibok sai kwatsam Jami'ar Amurka Ta Najeriya ko AUN ta waiwayesu da idon rahama

Wasu ‘Yan Matan Chibok Sun Shiga Sabuwar Rayuwa a Jami’a

Yayin da aka kai samame a makarantarsu dake garin Chibok ta jihar Borno cikin watan Afrilun bara. wasusnsu sun boye. Wasu kuma dirowa suka yi daga motar akori kura da aka sakasu. Wasunsu kuma arcewa kawai suka yi daga hannun ‘yan Boko Haram wadanda suka cinna wa makarantarsu wuta. To saidai ‘yanuwansu fiye da dari biyu ne ‘yan ta’adan suka wuce dasu kuma har yau babu duriyarsu ko inda suke.

Kodayake ‘yan mata 57 sun kubuta yau kusa da shekara daya ke nan babu wanda ya san inda 219 suke. Wadan nan ‘yan matan da suke tsira sun kasance a garin Chibok babu abun yi babu kuma begen zasu cigaba da karatu domin ‘yan Boko Haram suna kai hari kan makarantu a kokarin da suke yin na kafa tsatsaurar shariar musulunci a arewacin Najeriya.

Bisa ga alamu kuma basu da zabi. Tamkar tasu ta kare ke nan. To amma ba zato ba tsammani sai Jami’ar Amurka ta Najeriya ko AUN ta shiga lamarinsu.

Wani maigadi a jami’ar da ‘yaruwarsa tana cikin wadanda suka tsira shi yayi magana da shugabar jami’ar dake Yola, Margee Ensign. Biyo bayan bayanin da yayi mata Ensign ta san yakamata ta yi taimako. Ta dalilin hakan ‘yan mata 21 cikinsu yanzu suna karatu a jami’ar dake Yola fadar gwamnatin Adamawa.

Kamar yadda Ensign tayi bayani ‘yan matan suna wani shirin karatu ne na musamman da zai taimakesu kammala karatun sakandare nasu. Idan sun ci, kuma sun ga dama suna iya cigaba da karatun jami’a a wurin.

Ensign tace “Manufar jami’ar itace ta kasance makaranta dake kawo cigaban al’umma dake kewaye da ita ta kuma kyautata rayuwarsu. Tace “Dalilin da ya sa muka daukesu ke nan muka kuma tallafa masu da basu ilimi kyauta domin suna cikin mutanen da suka fi tagayyara a duk yankin” Ta cigaba da cewa “Sun sha muguwar azaba amma duk da haka sun fi kowadan ne dalibai da muka taba aiki dasu jajircewada son cigaba da karatu.

Cafke daliban Chibok ya jawo hankalin duniya kan kungiyar Boko Haram da kuma irin ukubar da al’ummar arewa maso gabashin Najeriya ke sha a hannun kungiyar.

Saidai kawo yanzu babu abun da ya canza zani a garin Chibok din tun da aka sace ‘yan matan a watan Afrelun bara. A watan Nuwamba ma sai da ‘yan ta’adan suka sake mamaye garin na dan wani lokaci kafin sojoji su fatattakesu.

Kamar yawancin jihohin arewa maso gabashin Najeriya, jihar Borno tana fama da mugun talauci da rashin cigaban al’umma. Duk da cewa garin nada mutane fiye da 66,000 titin da ya hada garin da sauran duniya bashi da kwalta.

Cikin wata fira da aka yi da ‘yan matan da suka tsira sun ce suna son su cigaba da karatunsu a AUN domin su taimaki Chibok.

Bisa ga umurnin AUN, Muryar Amurka ba zata ambaci cikakkun sunayen ‘yan matan ba.

Grace wadda take son ta zama likita tace talaucin al’ummarsu ya sa tana son tayi karatu. Tace “A akasarin gaskiya ina son kawo canji musamman domin bamu da hanya lamarin da ya sa sufuri nada wuya. Zuwa wurare na yi mana wuya. Muna son mu canza yankinmu.

Yana tace abun da ya fi bata wuya game da zuwa karatu a Yola shi ne barin iyayenta a Chibok. Tace “Abu ne mai wuya iyaye su rabu da ‘ya’yansu to amma sabili da batun cigaba ne dole muka daure”

Yana ta son tayi ilimin ma’adanan kasa. Amma ta san kome ma ya faru zata sake komawa Chibok.

Tace “Ina son in zauna a Chibok ko bama na din-din –din ba. Amma zan zauna a garin domin gari nan ne. Idan kuma har ina son na kawo canji dole ne na zauna cikin garin”

Bayan da ‘yan matan suka isa AUN daliban jami’ar sun yi maci a harabar jami’ar suna bukatar a sako sauran ‘yan matan Chibok din. Da aka soma macin ‘yan matan sai suka barke da wakar nan ta “bring back our girls. Da macin ya cigaba sai wakar ta sauya suna cewa “muna kewar ‘yan matanmu” kana suka karkare da “muna kaunar ‘yan matanmu”

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG