A Najeriya, madugun kungiyar Boko Haram ya kira annobar cutar COVID-19 wani yaki da kasashen duniya ke yi da Musulunci. A Iraq da Syria, ‘yan kungiyar IS sun bayyana annobar a matsayin wani horo ga makiyansu, a daidai lokacin da mayakan Shi’a da Iran ke goyon baya ke ba jama’a takunkumin rufe hanci da baki kyauta da kuma bayanai akan lafiyar al’umma.
Daga nahiyar Afrika zuwa Gabas ta Tsakiya, Turai da wasu yankunan, annobar cutar COVID-19 ta sa kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi maida martini ta hanyoyi dabam daban a yayin da suke kokarin karfafa matsayinsu don su sami galaba kan makiyansu. A Yau, wasu kungiyoyi na kiran annobar wani horo daga Allah akan makiyansu, wasu kalilan kuma na kallonta a matsayin wata dama da za su yi amfani da ita wajan daukar sabbin mayaka.
A Najeriya, madugun ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya saki wani bidiyo a watan Afirilun da ya gabata, inda ya bayyana matakin da kasashen duniya suka dauka akan annobar a matsayin wani yaki da musulunci da kasashen duniya ke yi. Shekau ya yi watsi da matakan kariyar kamar yin nesa-nesa da juna, ya na ikirarin cewa Musulmai na da kariya daga cutar coronavirus.
A watan da ya gabata shugaban shirin samar da zaman lafiya na majalisar Dinkin Duniya Jean-Pierre Lacroix ya gargadi kwamitin sulhun Majalisar kan cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda a Afrika, musamman a yankin kudu da hamada, na yunkurin yin amfani da lokacin annobar don yin barna a kasashensu da kuma dagula wa gwamnatocin kasashen lissafi. A misali, a watan Maris mayakan sa-kai a Mali sun kame shugaban babbar jam’iyyar adawa yayin da ‘yan Boko Haram suka kashe dakarun Chadi guda 92.
Facebook Forum