Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 235 a Wani Masallacin Juma'a a Masar


Masar
Masar

Jami’n tsaro a Masar sun ce wasu yan bindiga sun kai hari a wani masallaci cike da mutane a yau Juma’a a yankin Sinai mai fama da fitina a arewacin kasar, suka kashe mutane 235.

Hukumomin sun ce masu tsatsauran ra'ayin sun auna masu goyon bayan rundunonin tsaro ne a masallacin al-Rawda dake cikin garin Bira-al-Abd dake yamma ga babban birnin lardin el-Arish.


Sun ce mutane hudu da suke cikin wata mota a gefen hanya sun bude wuta a kan masu ibada a sallar Juma’a.


Shedun gani da ido sun ga motocin daukar marasa lafiya suna jigilar wadanda harin ya rutsa da su zuwa asibitocin dake kusa.


Galibi Yan bindigan sun fi auna jami’an tsaro a hare-haren da suke kaiwan, sai dai sun yi kokarin fadada hare haren zuwa wasu sassan kasar, ind a suka kai hari kan majami'u da masu ziyarrar ayyukan ibada.


Rundunonin tsaron Masar suna fama da yaki da kungiyar IS a yankin arewacin Sinai, inda yan bindigan suka kashe daruruwar yan sanda da sojoji tun lokacin da fada ya zafafa a wannan yanki shekaru uku a baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG