Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Sojojin Pakistan, Suka Kashe Biyu


Wannan shine hari na biyu da aka kai a kan jami'an tsaro a yankin Waziristan a wannan watan.

Wasu 'Yan bindiga sun kai wa ayarin rudunar sojin Pakistan hari yau Talata a wata karkara dake yankin Waziristan ta Arewa, suka kashe sojoji akalla biyu.

A wata gajeruwar sanarwa an bayyana cewa wani jami'in soja mai matsayin lieutanant na daga cikin wadanda suka mutu. a cewar su hakan ya faru ne yayin da yan bindigar suka harbi motar sojojin a cikin duwatsu inda ake yawan samun tashin hankali a yankin dake iyaka da Afghanistan.

'yan haramtaciyar kungiyar taliban ta pakistan sun dauki alhakin mummunan harin da aka kai wanda ya jikatta sojoji shida.

Wannan shine hari na biyu da aka kai a kan jami'an tsaro a yankin Waziristan a wannan watan. A satin da ya gabata ne wani bomb da aka boye cikin wani mashin dake ajiye a gefen hanya, ya tashi a lardin Mir Ali, wanda ya kashe mutane shida tare da jikkata mutane takwas, uku daga cikin wadanda suka mutu na shirin zama sojoji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG