'Yan matan su hudu sun fito ne daga wasu kauyuka kuma suka tada bamabamai a wajen binciken ababen hawa a kokarin da suka yi na kutsawa cikin birnin Maiduguri ta hanyar garin Mapa.
Lamarin na jiya ya zama karo na biyu da ake samun masu tada bamabamai a wannan hanyar shiga Maiduguri domin ko a watan jiya an samu tashin bamabamai a wurin.
Tashin bamabaman na jiya ya hallaka wani matashi da ake kyautata zaton dan kungiyar kato da gora ne da aka fi sani da suna Civilian JTF. Ya gamu da ajalinsa ne lokacin da daya daga cikin 'yan matan ta tada bam dake jikinta. Sauran ukun kuma sun yi yunkurin kutsawa cikin garin da karfi amma sai bamabaman dake jikinsu suka tashi. Su kadai suka mutu babu wanda bam dinsu ya kashe.
Alhaji Muhammed Kanar shi ne shugaban hukumar samarda agajin gaggawa na jihar Borno yayi karin haske akan lamarin.
Yace banda dan Civilian JTF da ya rasa ransa babu wanda ya mutu kuma saidai mutane biyar da suka jikata wadanda yanzu suna asibiti.
Matan yara ne kanana irin wadanda ake daukansu daga kauyukansu ana nada masu bamabamai a turasu su je su tayar. Shekarunsu ba zai wuje sha daya ko sha uku ba.
Ga karin bayani.