Kwamitin da gwamnatin jihar Filato ta kafa don yin bincike da gano maganin cutar coronavirus ya ce ya na da yakinin zai samar da maganin cutar.
Kwamitin mai mambobi 13 daga sassan binciken magunguna na zamani, da itatuwa, da tsirrai, da kwayoyin cuta, da kuma kwayoyin hallitar bil’adama, kwarrau ne da suka dade suna gudanar da binciken magunguna.
Shugaban kwamitin, Farfesa Noel Wanang, da ke sashen binciken magunguna da sinadarai masu guba a Jamiar Jos, ya ce suna fatan samun nasarar dakile cutar coronavirus. Ya kuma ce zasu tabbatar da cewa maganin da za su hada bai da illa ga bil’adama kuma zasu fara gwajin maganin akan dabbobi.
Tun farko gwamnan jihar Filato Simon Lalong ne ya umurci kwamitin akan ya nemo maganin cutar ko ta hanyar binciken magungunan zamani ko daga tsirrai. Ya kuma ce kwamitin ya tsara hanyoyin magance cutar, su kuma gudanar da gwajin maganin.
Wasu kwararru a fannin maganin gargajiya, Evangelist Joel Hamajulde Gashaka da Dakta Mohammad Ibrahim Jarawa sun ce tuni suka mika wa ma’aikatar lafiya ta tarayya magungunan da suka sarrafa na jinyar cutar coronavirus don a tantance su.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum