Wasu jamiaan aikin hadin gwiwa dake aiki a kasar Syria, daya Ba-Amurke daya kuma dan kasar Birtaniya sun hadu da ajalin su a sakamakon tashin wani Bomb a bakin hanya a ranar alhamis da daddare, Inji jamiaan kasar Amurka dake kasar, suka ce haka kuma wasu biyar sun samu rauni duka sakamakon wannan tashin bomb din.
Wasu daga cikin jamiaan kasar Amurka da basu yarda a ambaci sunayen su ba sun shaidawa kanfanmin dillacin labrai na Reuters cewa an kai wannan harin ne a birnin Manbij dake arewacin Syria.
Sai dai bayanan farko da ya fito daga sojojin Amurka bai nuna ainihin inda aka kai wannan harin ba, haka kuma basu bayyana sunaye da kasashen wadanda wannan lamari ya rutsa dasu ba, sai dai kawai suka ce maaikatan hadin gwiwa ne.
Mai Magana da yawun sojojin na Amurka Conel Ryan Dillion bai bayyana nan take su wanene keda alhakin kai wannan harin ba amma yace tuni suka tantance binciken su akan wannan harin kuma ba zasu bayyana shi ba a halin yanzu har sai sun kammalla bincike.
Facebook Forum