Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Asibitoci a Afirka Ta Kudu Na Kin Karbar Masu COVID-19


Wani likita da mai jinya a wani asibiti da ke Afirka ta Kudu
Wani likita da mai jinya a wani asibiti da ke Afirka ta Kudu

Wasu asibitoci a Afirka ta Kudu sun ki karbar daruruwan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus saboda rashin wadatattun ma’aikata da kayakin aikin. 

Dr. Tobisa Fodo, ta ce rubu’in marasa lafiyan ne kawai sashin kulawa ta musamman a asibitinta dake Port Elizabeth ya iya karba.

Dr. Fodo ta ce, "na kan damu idan nayi la’akari da yadda ni da abokan aiki na zamu dubi tsabar idanun mahaifiyar wani, mahaifin wani, kakar wani ko kawun wani mu ce musu ba za mu iya ba." Mutane da dama suna mutuwa a Afirka ta Kudu ba tare da samun kulawa ba.

Afirka ta Kudu ta tabbatar da adadin wadanda su ka kamu da coronavirus sama da dubu dari uku, kana sama da mace-mace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG