Bayan ya karbi 'yan matan Chibok 82 da kungiyar Boko Haram ta sako tare da yiwa 'yan Najeriya gargadin cewa su guji shan magani ba tare da izinin likita ba, shugaba Buhari ya mika ragamar mulkin kasar Najeriya ga Mataimakinsa Farfsa Yemi Osinbajo kamar yadda doka ta tanada kana ya kama hanyar zuwa Birtaniya ganin likitocinsa.
Ministan Shari'a Barrister Abubakar Malami ya gana da shugaban kafin ya tashi. Ya nuna jikin na shugaban nada sauki. Yana cikin koshin lafiya sai dai fata ga Allah shi ne ya kara samun karfin jiki, inji Abubakar Malami.
Shi ma masanin shari'a Yusuf Sallau Mutum Biyu yana ganin addu'a ga shugaban ne mafi a'ala tunda dai ya bi ka'idar doka. Ya jawo hankalin mutanen dake maganganun da basu dace ba dangane da rashin lafiyar shugaban da su daina.
Yana mai cewa kamar yadda aka sani kowane mutum a duniya na iya kamuwa da rashin lafiya kuma zai iya zuwa asibiti neman magani. Shugaba Buhari, injishi, mutum ne dan Adama kaman kowa, musamman kasancewa shekarunsa sun haura saba'in. Duk wanda ya haura shekarun ana ganin akwai yi wuwar wata rana zai iya kwantawa rashin lafiya. Yace wannan ba zai zama uzurin da za'a dinga siyasa dashi ba. Yace akwai wasu ma suna cewa ya ajiye mulki. Addu'a ya kamata a dinga yi masa a wannan lokacin.
Isa Tafida Mafindi yace shugaba Buhari ya kawo nasara a Najeriya. Yace abubuwa da yawa suka bayyana da suka nuna cewa Najeriya kasa ce dake bukatar shugabanci kuma ta samu. Yace dama can Shugaba Buhari yayi alkawarin yin abubuwa uku. Zai kawo tsaro. Zai farfado da tattalin arziki. Zai habaka ayyukan noma Yayi misali da yadda ayyukan noma suka habaka.
Fadar shugaban kasa tace likitoci ne zasu ayyana wa'din da shugaban zai yi a Ingila.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum