Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sabon Rikici Yana Tashi Tsakanin Amurka Da China


Shugaba Trump na Amurka da Xi Jin Ping na China
Shugaba Trump na Amurka da Xi Jin Ping na China

Wannan lamari ya biyo bayan umarnin da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama na China ya dauka na umarni ga kamfanonin jiragen sama masu jiglar fasinja na sauya yadda suke kallon Taiwan, da Hong Kong da Macau.

Fadar White House ta shugaban Amurka jiya Asabar ta soki kasar China da kakkausar lafazi kan yunkurin kasar ta Sin na tilastawa kamfanonin jiragen sama na Fasinja su sauya yadda suke daukar Taiwan, da Hong, da Macau, a zaman kasashe masu zaman kansu.

A dai-dai lokacinda kasashen biyu suke jani-in-jaka ta fuskar kasuwanci, gameda rarar da China take da samu, fadar ta White House tace hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta China, ta aike da wasika ga kamfanonin jigilar fasinja ta sama na kasashen ketare 36 ta bukaci su aiwatar da canji a shafukansu a internet.
Taiwan ce lamari mafifi sarkakiya. China tana kallon yankin mai tafiyarda al'amuranta kai tsaye a zaman fandarariyyar lardi.

Amma Hong Kong da Macau da suka kasance karkashin mulkin mallaka yammacin duniya, yanzu sun koma hanun China, kodashike suna ci gaba da tafiyarda harkokin su duk da kasancewa karkashin China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG