Mamadou Wade Diop wanda ya shafe shekaru ya na amfani da kananan jirage marasa matuki wajen daukar hotuna da kuma fannin kiwon lafiya, yanzu ya kera karamin jirgi maras matuki da hadin gwiwar makeran gargajiya a kasar Senegal.
Diop wanda ya ke kiran kanshi da suna Dakta Drone a kafofin sada zumunta, ya kasance daya daga cikin kalilan mutane masu gyaran kananan jiragen a birnin Dakar.
Amma a baya-bayan nan, ya dauki wani matakin ci gaba, inda ya ke tuntubar masana dake kera jiragen a fadin duniya, kan yadda zai kirkiri nashi jirgin.
Diop ya ce, ya na ganawa da masu kera jiragen a kasashe irin su Faransa da China ta yanar gizo, domin jin irin tasu basirar domin samun hanyar da zai kirkiri na shi jirgin.
Sai dai Diop, ba ta nan kadai ya kware ba, yana aiki a bangaren hada sauti da hotunan bidiyo, inda ya ke bayar da hayar kananan jiragensa masu dauke da kamarar daukar hoto ga manema labarai da masu hada shiri kan wani abu na tahiri a wasu yankunan Senagal.
Dalilin da yasa zai kera wannan jirgi nashi, shine domin ya ba da gudumawa ta bangaren Kiwon lafiya. Jirgin zai kasance yana feshin wani sinadarin magani domin hana sauraye su hayayyafa a cikin ruwa.
Sai dai wata matsala daya ita ce, ba dukkan kayan da ake bukata wajen hada kananan jiragen za a iya samu a kasar Senegal ba, amma Diop yace yana son ya nuna cewa abu ne da zai iya yiwuwa a kirkiri wannan fasaha a kasar sa ta haihuwa wato Senegal.
Diop ya ce yana sayen wasu kayayyakin da yake amfani da su daga kasar China, kuma yana aiki tare da makera domin samun karafunan da yake bukata.
Facebook Forum