Rundunar sojojin Najeriya ta ce wani madugun tsagera a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur ya mika sansanoni guda 8 ga hukumomi. Ateke Tom ya mika wadannan sansanoni dake cikin Jihar Rivers ne a cikin ‘yan kwanakin da suka shige. Ateke Tom yana daga cikin shugabannin tsageran da suka yi na’am da ahuwar da gwamnati ta yi musu da nufin wanzar da kwanciyar hankali a yankin na Niger Delta mai fama da fitina. Hare-hare da sace-sacen mutane da ake yi a yankin, musamman a kan masana’antar, sun rage yawan man da Najeriya ke hakowa da kudaden shugar da take samu a cijkin ‘yan shekarun nan. Rundunar sojoji tana ci gaba da kai farmaki a kan tsageran da suka ki yarda da shirin ahuwar. A cikin wannan watan, sojoji sun kai farmaki a kan wasu sansanoni uku na wani madugun tsagera da ake kira John Togo. Shaidu da kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce an kashe fararen hula da dama a fadan. Togo dai ya tsere ba a kama shi ba. A watan da ya shige ma, sojoji sun kai farmaki a kan sansanonin wani madugun tsagera mai suna Obese inda suka kwato mutane 19 da aka yi garkuwa da su.
Wani madugun kungiyar tsagera Tom Ateke ya mika sansanoni takwas ga jami'an tsaro

Wani madugun kungiyar tsagera a yankin Niger Delta Tom Ateke ya mika sansanoni takwas ga jami'an tsaro.