Wani bayanin asiri da aka tona na diplomasiyar Amurka ya nuna wani kalami da aka ce anji yana fitowa daga bakin shugaban Nigeria na yanzu, Goodluck Jonathan, inda yake bayyana cewa shi yayi imani, fitowarsa daga yankin Niger delta ce kawai tasa aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasa a 2007, ba wai wata kwarewarsa ta siyasa ba. Wannan bayanin asirin da cibiyar tonon assiran nan ta duniyar gizo ta Wkileaks ta bankado, ya bayyana cewa wannan maganar anyi tane tsakanin shi Mr. Joanthan da tsohuwar jakadiyar Amurka a can Nigeria, Robin Sanders. Bayanin yace Mr. Jonathan da bakinsa ya fadawa jakadiyar cewa shi ya san ba wai an zabe shi a matsayin VP ne don shi wani gwaninta yake da ita , ta siyasa ba, don ya san bai iya wata siyasa mai yawa ba. Ya kuma ce ya san akwai mutane da yawa da suka fi shi kwarewa a harakar siyasar.
Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa, yana ganin fitowarsa daga yankin Niger Delta ita ce tasa aka bashi mataimakin shugaban kasa a 2007.