Wani munmunan hadarin jirgin ruwan kwale-kwale da ya nutse da jama'a, a garin Tsibiri na jihar Maradi a jamhuriyar Nijar, yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 11, an samu nasarar tsamo wasu uku da suka jikkata. Jami'an kwana-kwana da 'yan sandan kungiyar jihar Maradi, suna ci gaba da neman sauran mutane da su kai batan dabo cikin gulbin.
Wasu shaidun gani da ido sun bada bayanin cewa, baza a san yawan wadan da suka mutu ba, ko suka bata a gulbin yanzu. Wasu kuma sun yi bayanin yadda suka kubuta daga wannan lamarin.
Shima gwamnan garin Zakari Umaru, daga jin wannan labarin, ya garzaya wajen, don ganema ido. Yayi jawabin cewa jama'a su dinga kiyaye abubuwan da suke daurawa a kan jiragen.
Ya kara da cewa baza a san adadin wadan da suka mutu ba, sai bayan an duba sosai. A yanzu dai, har an fara shirin jana'izar wadan da suka rasu.
Ga rahoton Tamar Abari.
Facebook Forum